Romans 16

Gaisuwa ta Kaina

1Ina gabatar muku da ʼyarʼuwarmu Fibi, baranyar ikkilisiya a Kenkireya. 2Ina roƙonku ku karɓe ta a cikin Ubangiji yadda ya dace a karɓi tsarkaka a kuma ba ta kowane irin taimakon da take bukata daga wurinku, gama ta zama mai taimako ƙwarai ga mutane masu yawa, haɗe da ni ma.

3Ku gai da Firiskila da Akwila, abokan aikina cikin Kiristi Yesu. 4Sun yi kasai da ransu saboda ni. Ba ni kaɗai nake musu godiya ba amma har ma da dukan ikkilisiyoyin Alʼummai.
5Ku kuma gai da ikkilisiyar da take haɗuwa a gidansu.
Ku gai da ƙaunataccen abokina Efenetus, wanda ya zama na farko a karɓar Kiristi a lardin Asiya.
6Ku gai da Maryamu wadda ta yi muku aiki tukuru.
7Ku gai da Anduronikus da Yuniyas, dangina waɗanda aka ɗaure a kurkuku tare da ni. Su fitattu ne sosai a cikin manzanni, sun riga ni zama masu bin Kiristi.
8Ku gai da Amfiliyatus, ƙaunataccena a cikin Ubangiji.
9Ku gai da Urbanus, abokin aikinmu cikin Kiristi, da kuma ƙaunataccen abokina Sitakis.
10Ku gai da Afelles wanda amincinsa cikin Kiristi tabbatacce ne.
Ku gai da iyalin gidan Aristobulus.
11Ku gai da ɗanʼuwana, Hirodiyon.
Ku gai da iyalin gidan Narkissus da suke cikin Ubangiji.
12Ku gai da Tiryifena da Tiryifosa, matan nan da suke aiki tukuru cikin Ubangiji.
Ku gai da ƙaunatacciyata Fersis, wata matan da ta yi aiki tukuru cikin Ubangiji.
13Ku gai da Rufus zaɓaɓɓe cikin Ubangiji, da kuma mahaifiyarsa, wadda ta zama kamar mahaifiya a gare ni.
14Ku gai da Asinkiritus, Filegon, Hermes, Faturobas, Hermas da kuma ʼyanʼuwan da suke tare da su.
15Ku gai da Filologus, Yuliya, Nereyus da ʼyarʼuwarsa, da kuma Olimfas da dukan tsarkakan da suke tare da su.
16Ku gaggai da juna da sumba mai tsarki.
Dukan ikkilisiyoyin Kiristi suna gaishe ku.
17Ina roƙonku, ʼyanʼuwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su. 18Gama irin waɗannan mutane ba sa bautar Ubangijinmu Kiristi, sai dai cikinsu. Ta wurin yaudara da kuma daɗin baki, suna ruɗin marasa wayo. 19Kowa ya riga ya ji game da biyayyarku, don haka ina cike da farin ciki game da ku; amma ina so ku zama masu hikima game da abin da yake nagari, ku kuma zama marasa laifi ga abin da yake mugu.

20Allah na salama zai tattake Shaiɗan ba da daɗewa ba yǎ kuma sa shi a ƙarƙashin sawunku.

Alherin Ubangijinmu Yesu kuma yǎ kasance tare da ku.

21Timoti, abokin aikina, yana gai da ku, haka ma Lusiyus, Yason, da Sosifater, dangina.

22Ni, Tertiyus, wanda ya rubuta wannan wasiƙa, ina gai da ku cikin Ubangiji.

23Gayus, mai masauƙina, mai kuma saukar da dukan ʼyan Ikkilisiya, yana gaishe ku.

Erastus, mai bi da ayyukan jamaʼa a birnin, da kuma ɗanʼuwanmu Kuwartus suna gai da ku.
Waɗansu rubuce rubucen hannu na dā gai da ku. 24 Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yǎ kasance tare da ku duka. Amin.


24
This verse is empty in this translation.
25Ɗaukaka ta tabbata ga mai ikon ƙarfafa ku bisa ga bisharata, bisa ga waʼazin Yesu Kiristi, wadda ta gare ta ne aka bayyana asirin nan da yake ɓoye tun filʼazal, 26amma yanzu kuwa aka bayyana, aka kuma sanar ta wurin rubuce rubucen annabawa bisa ga umarnin Allah madawwami, domin dukan alʼummai su gaskata su kuma yi masa biyayya—  27ɗaukaka ta tabbata har abada ga Allah, wanda shi ne kaɗai mai hikima ta wurin Yesu Kiristi! Amin.

Copyright information for HauSRK